On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Kama Karin Mutane 57 Da Sace Kayyaki A Wuraren Da Gwamnatin Kano Ke Aikin Rusau

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano ta sake yin nasarara kama wasu mutane 57 da ake zargi da fasa shagunan mutane ta hanyar amfani da aikin rusau da gwamnatin jihar ke gudanarwa.

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa shine ya tabbar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce kamen cigaba ne akan mutane 49 da aka kama aka gurfanar da su a gaban kotun majistare mailamba 35 dake Normans Land a Kano, bisa laifukan da suka hada da barna da fasa shaguna da sata.

Ya kara da cewa karin mutanen 57 za’a gurfanar da su a gaban kotu da laifuka iri daya wanda ya kai jimla zuwa mutane 106.

Sanarwar ta shawarci wadanda abin ya shafa da su je sashin binciken manyan laifuka (SCID) dake shalkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano a Bompai, domin bayar da shaida kan laifuka daban-daban da wadanda ake zargin suka aikata, ko ta wannan lambar waya, 0803 824 94553.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, ya yaba wa wadanda suka taimaka da bayanan da suka kai ga kamawa da kuma kwato dukiyoyin da aka sace.

Ya nanata cewa aikin ‘yan sanda wani nauyi ne na hadin gwiwa don haka ya yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su gargadi matasa su daina wawure dukiyar jama’a, saboda duk wanda aka kama zai fuskanci fushin doka.

A ci gaba da aiki da dabarun da aka samar domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar Kano, kwamishinan ‘yan sandan, ya bayar da umarnin gudanar da sintiri ba dare ba rana biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu batagari fakewa da aikin rushe  gine-gine da gwamnatin jihar Kano ke yi wajen wawure dukiyar jama’a.