‘Yan Ta’adda sun yiwa Ayarin motocin jami’an dake tarbar shugaban kasa harin kwantan ‘bauna, tawagar jami’an sun hada da jami’an tsaro da ‘yan Jarida da kuma masu tsara harkokin tarbar baki na fadar shugaban kasa.
Harin kwantan baunar da ‘Yan Ta’adda suka kaddamar a kusa da garin Dutsinma dake jihar Katsina yayi sanadin mutuwar jami’an yansanda biyu. Fadar shugaban Kasa ta baiyana cewa tawagar ayarin jami’an dake tarbar shugaban kasar na kan hanyarsu ne ta zuwa Daura Mahaifar shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda zai je can domin yin Idin Babbar Sallah, amma shugaban kasar baya cikin ayarin.
Babban Mataimaki na Musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada Labarai da kuma wayar da kai, Malam Garba Shehu ya tabbatar da kai harin ta cikin wata sanarwa da ya fitar, Yace Maharan sun yiwa ayarin jami’an dake tarbar shugaban kasar kwantan bauna, tare da bude masu wuta babu kakkautawa, sai dai kuma sojoji da jami’an yansanda da kuma jami’an tsaron farin kaya na DSS dake cikin tawagar sun dakile harin.
Garba Shehu ya baiyana cewa mutane biyu ne kadai suka samu ‘yan raunika, To sai dai Kakakin Rundunar Yansandan Jihar Katsina, Gambo Isah a wata sanarwa da ya fitar, Yace Baturen Yansandan yankin tare da wani mutum daya na daga cikin wadanda aka halaka a yayin harin kwantan baunan.