Nan kuma an jiyo karar fashewar wasu abubuwa da kuma harbin bindiga a kusa da Gidan Gyaran Hali na Kuje dake Abuja babban birnin taraiyya a daren jiya.
Duk da cewar har yanzu akwai ‘kanfar cikakken bayanin abunda ya faru, sai dai mazauna yankin sun fadawa manema Labarai cewa, harbin bindigar ya shafe tsawon mintina 20.
Mazauna yankin sunyi fargabar cewa, Yan Bindiga ne suka kaiwa gidan gyaran halin farmaki.
A yanzu haka Hukumar kula da Gidajen Gyaran Hali ta kasa ta tabbatar da harin da aka kai, kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Abubakar Umar ya fitar.
Sanarwar tace wasu ‘yan ta’adda da ba’a san ko su waye ba sun kaiwa gidan gyaran hali na kuje hari da karfe 10 na dare, sai dai kuma jami’an tsaro sun samu nasarar dakile harin.
Kazalika yace a yanzu haka an samu dawowar zaman lafiya, inda yayi alkawarin fitar da cikakkun bayanai akan harin nan bada jimawa ba.