Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kafa kwamitin fadar shugaban kasa kan sauya Fasalin harkar kiwon dabbobi a Najeriya.
Ana kuma dorawa kwamitin alhakin samar da hanyoyin magance rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a fadin Najeriya na tsawon lokaci.
Hakan ya biyo bayan mika rahoton taron kasa kan sauye-sauyen harkokin kiwon dabbobi da magance rikice-rikicen da ke faruwa a Najeriya ga shugaban kasar a ranar Alhamis.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Gwamnan Kano, AbdullahiUmar Ganduje ne ya jagoranci taron, inda ya tunatar dabcewa a lokacin da yake Gwamna ya karbi bakuncin taron kasa ne domin tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin manoma da makiyaya.
Daga nan Shugaban kasa ya bukaci kwamitin da ya hada hannu da ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya, domin samar da hanyoyin magance tashe-tashen hankulan.