Shugaban kasa Bola Tinubu ya rushe hukumar gudanarwar aikin Hajji ta kasa NAHCON, kamar yadda wata sanarwa da mai Magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ta baiyana.
Sanarwar ta baiyana Jalal Ahmad Arabi a matsayin sabon shugaban hukumar aikin hajji ta kasa wanda zai jagorance ta nan da tsawon shekara hudu.
Shi kuwa shugaban hukumar mai barin gado Alhaji Zikirullah Kunle Hassan an bashi umarnin tafiya hutun ritayar aiki na tsawon watanni ukku farawa daga yau Laraba.
Kazalika Jalala Arabi zai fara aiki daga yau a matsayin mukaddashin shugaban hukumar aiki hajji ta kasa , a yayin da zai zama cikakken shugaban hukumar mai daga ranar 17 ga watan Janairun bana.