On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

An Kaddamar Da Kwamitin Sasanta Al'umma A Masarautar Gaya Dake Kano

Masarautar Gaya dake jihar Kano ta kaddamar da wani kwamiti mai mutane 9 domin daukar gabarar sasantawa da sulhu a tsakanin al’umma.

Da yake jawabi yayin kaddamar da kwamitin mai martaba Sarkin Gaya Alh. Dr, Aliyu Ibrahim Abdulkadir yace an dauki mataki ne domin shiga tsakani tare da sulhunta duk wata matsala ta zamantakewa da nufin rage yawan kararraki da ake shigarwa bana kotuna.

Dr. Aliyu Ibrahim  ya hori ‘ya ‘yan kwamitin da su tabbatar da kwarin gwiwar da ake da ita akansu a aikace, inda ya umarcesu da suyi aiki da masu rike da mukaman gargajiya domin samun nasara.

Har Ila yau yace za’a kaddamar da irin wannan kwamiti a garuruwan hakimai da dagatati da kuma masu Unguwanni.

Sarkin ya ayyana Mallam Kabiru Lamido Wudil amatsayin shugaban kwamitin na Sasanta Jama’a sai Farfesa Annan Garba Gaya amatsayin Sakatare.