An jibge jami’an tsaro daga bangarori daban daban a Abuja babban birnin taraiyya a jiya, Gabanin hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, zata yanke yau, akan masu kalubalantar nasarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya samu a zaben da ya gabata.
An baza jami’an Yan sanda masu kwantar da tarzoma da Jami’an hukumar tsaro ta CIVIL DEFENCE da sauran jami’an hukumomin tsaro a harabar kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da sauran wasu muhimman wurare dake Abujar.
Da safiyar yaune za’a yanke hukuncin karkashin mai shari’a Haruna Tsammani da tallafin Alkalan kotun, Stephen Adah da Monsurat Bolaji da Mai shari’a Moses Ugo da kuma Alkali Abba Mohammed.
Hakan dai na zuwa ne a yayin da dubban magoya bayan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour, Da na Bola Tinubu na jam’iyyar APC ke dakon ganin yadda hukuncin zai kaya da safiyar wannan rana.