Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum Ya yiwa manoman jihar bayanin dalilan da suka sa aka hana amfani da takin zamani samfurin Urea da kuma NPK a fadin jihar.
Yace babu dalilin da zaisa a rika amfani da nau’ikan takin a fadin jihar, kasancewar tun tuni ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya haramta yin amfani dashi.
Yace ofishin mai bawa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro ya haramta yin amfani da takin zamani samfurin Urea da kuma NPK ne,kasancewar mayakan tada kayar baya suna amfani dasu wajen hada Bam.
Gwamnan ya baiyana haka ne a ranar Laraba lokacin da yayi rangadin wasu gonaki 10 dake wajen wasu kananan hukumomi hudu na jihar, wanda suka hada da Maiduguri da Jere sai Mafa da Dikwa domin duba yadda suke gudanar da harkokin nomansu.
Gwamnan ya kara da cewa wannan shine dalilin da yasa ya bada umarnin raba kayan aikin gona cikinsu da Tan-tan ga manoma jihar domin inganta aiyukansu.