Majalisar dattawan Amurika ta amince da kudirin dokar nan da ake cece kuce kansa na haramta yin amfani da shafin TikTok.
Majalisar ta baiwa mai kamfanin dan kasar China Byete Dance wa’adin watanni tara da ya siyar hajojinsa dake kan shafi ko kuma a kulle shi baki daya a kasar ta Amurika.
A yanzu an mika kudirin dokar ga shugaba Joe Biden wanda y ace zai rattaba mata hannu da zarar ta riski teburinsa na shugaban kasa.
Idan har Amurika ta samu nasara wajen tilasta mai kanfanin na TikTok siyar das hi, hakan zai sa duk wata yarjejeniya da za’a yi dole ne sai da amincewar kasar China, kuma kasar ta lashi takobin sukar matakin.