A yayin da ake cigaba da kidaya kuri’ar zaben shugaban kasa a kasar Kenya wanda aka yi a ranar Talata, A yanzu haka an hana gidajen Talabijin na kasar cigaba da gabatar da sakamakon zaben kai tsaye.
Kwana daya bayan zaben ne, Gidajen Talabijin na kasar suka fara gabatar da sakamakon zaben kai tsaye, sai dai kuma an samu shakku kan yadda suke gabatar da sakamakon.
Wasu alkaluma sun nuna cewa an samu rata tsakanin biyu daga cikin ‘yan takarar shugaban kasar Kenya, wanda ya hada da Raila Odinga wanda yake samun goyon bayan shugaban kasar, da kuma Mataimakin shugaban kasar mai barin gado William Ruto.
A yanzu haka hukumar zaben kasar tana da wa’adin nan da ranar 16 ga watan da muke ciki domin sanar da sakamakon karshe na zaben, wanda zai nuna wanda zai gaji buzun shugaban kasar Uhuru Kenyatta wanda ke kan gadon mulki tun shekarar 2013.