An fara rufe cibiyoyin kiwon lafiya Na sha Ka Tafi a wasu jihohin Amurka bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke a ranar Juma'a na soke 'yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya baiwa matan Amurka na zubar da ciki.
Kimanin rabin jihohin ne ake sa ran za su gabatar da sabbin takunkumi akan matakin bayan kotu ta soke hukuncin da ta yanke na shekaru 50 na Roe v Wade wanda ya halasta zubar da ciki, A yanzu haka Jihohi 13 sun haramta zubar da ciki nan take tun bayan sanar da hukuncin.
Sai dai kuma, Shugaban kasar Amurika Joe Biden ya bayyana hukuncin a matsayin wani abu mai rudani da tayar da hankali.
A yanzu haka an fara zanga-zanga a wasu biranen Amurka domin nuna adawa da hukuncin.