An kashe wani kasurgumin jagoran ‘yan ta’adda, Abdulkarim Faca-faca, wanda ake zargin yana cikin wadanda suka kitsa kai harin kan ayarin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina a lokacin hutun Sallah da ya gabata.
Rahotanni sun ce an kashe Abdulkarim a ranar Asabar tare da wasu ‘yan kungiyarsa su takwas a wani hari da rundunar sojojin sama ta kasa ta kai ta sama a lokacin da suka kai farmaki kan wasu ‘yan ta’adda a kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana.
A cewar rahoton, da yawa daga cikin 'yan ta'addar sun samu raunuka sanadiyar harbin bindiga, amma sun yi nasarar tserewa.
(Karin Magana:....Gidan Zuma ba Kasuwa ba ce)
Dan majalisa mai wakiltar Safana a majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Abduljalal Haruna Runka, ya tabbatar da rahoton.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isah shi ma ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.