Wata Kotun Majistare da ke Kano a ranar Litinin ta bayar da umarnin tsare wani mutum da ake zargi dauke da katin zabe na dindindin guda 29 a Kano.
An tuhumi wanda ake zargin, Tasi’u Abdu da mallakar katinan zabe namutane daban-daban.
Tun da farko, lauyar masu shigar da karadaga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Badiyya Lawan, ta shaidawa kotu cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Janairu.
Tayi zargin cewa an kama wanda ake kara ne da katinan zabe guda 29 na mutane daban-daban ba tare da bayar da gamsasshen bayani kan yadda ya samu katunan ba.
Wanda ake kara, ya ki amsa laifinsa.
Daga nan Babban alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 30 ga watan Janairu, domin yanke hukunci kan neman belinsa.