Jihar Neja ta gudanar da jana’izar mutane 10 da hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a ranar Alhamis din da ta gabata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Cikin wadanda abin ya shafa har da yara takwas.
Hotunan da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja ta fitar a ranar Litinin, sun nuna cewa an binne yaran ne a wani babban kabari mai girma.
Idan dai za a iya tunawa, mutane 34 ne da suka hada da kananan yara 10 na cikin kwale-kwalen wanda ya kife a yayin da suke tafiya a karamar hukumar Shiroro a ranar Alhamis din makon jiya.
Da yake karin haske a ranar Litinin, Daraktan hukumar bauarbAgaji NSEMA, Salihu Garba ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa, kadawar igiyar ruwa mai karfi da kuma bishiyoyi ne suka haddasa kifewar jirgin.