Alamu sun bayyana cewa har yanzu Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta ce komai ba game da dage haramcin biza da aka kakabawa matafiya daga Najeriya a cikin sanarwa a hukumance bayan shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya sanar da cewa ganawar da Tinubu ya yi da mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa, ta warware takaddamar da ke tattare da hana ‘yan Najeriya biza watanni 10 da suka gabata da kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen Etihad da Emirates.
Ngelale ya kara da cewa, bisa wannan yarjejeniya mai cike da tarihi, kamfanonin jiragen saman Etihad da na Emirates za su gaggauta dawo da jadawalinsu na tashi da saukar jiragen sama, ba tare da wani bata lokaci ba.
Sai dai sanarwa mai sakin layi goma da mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa suka fitar jim kadan bayan kammala taron kuma kamfanin dillancin labaru na Emirates, ya rawaito, babu wani sharhi game da dage haramcin bizar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito Kamfanin Dillancin Labarai na Hadaddiyar Daular Larabawa na cewa, Al Nahyan ya bayyana fatansa ne kawai cewa shugabannin biyu za su yi aiki tare domin karfafa alaka tsakanin Daular larabawa da Najeriya domin amfanin kasashen biyu.