‘Yan sa’oi bayan sanarwar da sabon shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya yi na cewar biyan tallafin mai ya zama tarihi a kasar nan, a yanzu haka an fara samun dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai dake Abuja da Legas da kuma wasu jihohin kasar nan.
Rahotanni sun baiyana cewar, Masu ababen hawa sun cika gidajen mai a Abuja da Nasarawa da jihar Naija da tsakar ranar jiya,tun bayan bullar sanarwar da sabon shugaban kasar ya fitar.
Kazalika alamu sunyi nuni da cewar, tun bayan kalaman sabon shugaban kasar, Masu ababen hawa suka fara rububin neman man fetir a gidajen mai dake Abuja da kuma makotanta.
Mafi akasarinsu sun cika tankin ababen hawansu, saboda fargabar janye tallafin man, wanda ake tsammanin litar man fetir zata haura naira 500.
To sai dai, Kungiyar Dillalan mai ta kasa mai zaman kanta IPMAN, ta soki matakin da sabon shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka na janye tallafin daga sabon watan Yuni da zamu shiga, kasancewar babu tanadin hakan a cikin kasafin kudi.
A martanin da kungiyar ta yi tab akin kakakinta, Ukadike Chinedu, ta ce kamata yayi sabuwar gwamnatin ta tattauna da ‘yan kasuwar mai kafin daukar irin wannan mataki.
Ya ce bai kamata a janye tallafin mai a kasar nan batare da gyara matatun man da ake dasu ba, To sai dai kuma kungiyar manyan dillalan mai ta kasa MOMAN, Ta soki lamirin inda ta ce ya kamata a janye tallafin man dungurun- gum.
Babban sakataren kungiyar,Clemen Isong, Ya ce Najeriya na asarar kudin shigar da take samu ta hanyar biyan makudan kudi da sunan biyan tallafin mai.