On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Dawo Da 'Yan Sandan Da Aka Kora Bakin Aiki Saboda Yin Harbi Lokacin Da Suke Rakiya Ga Mawaki Rarara

Babban Sufeton rundunar ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin mayar da jami’an ‘yan sanda uku bakin aikinsu biyo bayan korarsu, a watannin baya sakamakon amfani da bindiga ba bisa ka’ida ba.

‘Yan sandan dake bada tsaro ga fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara sun hadar da Sufeto Dahiru Shu’aibu da Sajan Abdullahi Badamasi da Isah Danladi da ke aiki da sashin tsaro na musamman na zone 1 da ke rundunar ‘yan sandan a jihar Kano, wadanda aka kora sakamakon yin amfani da bindiga ba bisa ka'ida bad a tsoratar da jama’a da kuma barnatar da harsashi.

Tunda farko rundunar ta ce, da suke bakin aiki a ranar 7 ga watan Afrilun 2023 a kauyen Kahutu, jihar Katsina, jami’an sun yi harbe-harbe a sama daga makaman aikinsu duk da tsarin aikin yan sanda bai yarda da harbi a iska ba, da kuma yin watsi da hatsarin da hakan zai iya haifarwa ga taron jama’ar da ke wajen harda yara. Wannan ba iya laifi da rashin sanin makamar aiki bane kawai harda tozarta rundunar da kasar baki daya."

Sai dai a wata sanarwa ranar asabar dauke da sahannun mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, Alkali Baba ya bayar da umarnin sauyawa jami’an da aka dawo da su bakin aiki, wuraren aiki daga yankin Arewacin Kasar nan zuwa kudanci cikin gaggawa.

CSP Olumuyiwa Adéjọbí, shine ya ce  jami’an sun daukaka kara  bisa korarsu  daga rundunar  ta ‘yan sandan.