Gwamnatin tarayya ta samu nasarar dawo da wasu ‘Yan Najeriya da suka makale da kuma wadanda aka tsare daga sansani daban daban na kasar Libiya, har guda 281 a ranar Talata.
Aikin dawo da mutanen ya kasance na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da kuma hukumar kula da ‘yan Gudun hijira ta majalisar dinkin duniya.
Jami’in kula da walwala na ofishin jakadancin Najeriya a kasar Libiya, Kabiru Musa ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya a Abuja.
Daga cikin mutanen da suka dawo, sun hada da ‘yan Najeriya 159 da aka sako daga gidajen yari daban daban na kasar Libiya, sai kuma ragowar 122 da aka samu suna ragaita a sassa daban daban na kasar.