Hukumar kula da shirin masu hidimtawa kasa ta fara aikin wayar da kan masu hidimitawa kasa kafin rarraba su zuwa wurare daban daban a karon farko, bayan shafe shekara 13 batare da gudanar da shirin ba, tun bayan da aka dakatar da shi a shekarar 2011, saboda matsaloli na rashin tsaro.
Jami’in kula da shirin a jihar, Mohammed Adamu a lokacin da yake jawabi yayin bukin rantsar da rukunin masu hidimtawa kasar a ranar Talata, ya jinjinawa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum saboda namijin kokarinsa wajen ganin an ci gaba da shirin a jihar.
An yiwa masu bautawa kasar sansani a kwalejin horas da malaman larabci dake jihar, wadda ke zama matsagunnin wucin gadi , a yayin da hadakar jami’an tsaro suka tsaurara tsaro a wajen.
Shima a nasa jawabin gwamna Zulum, ya baiyana farin cikinsa wajen ganin dawowar shirin, inda ya ce yunkurin ya sake tabbatar da dawowar zaman lafiya da tsaro a jihar bayan shafe shekaru da dama tana fama da matsalar mayakan tada kayar baya.