An gurfanar da sojoji 227 da ke yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan a gaban wata kotun hukunta lefukan soji ta musamman da rundunar soji ta kafa, bisa aikata laifuka daban-daban na rashin da’a.
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da wata kotun wadda za ta yi shari’ar sojoji 29 a shalkwatar rundunar dake Maimalari a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Ya ce an bada shawarar sallamar wasu sojoji 4 sannan kuma za a daure wasu 30 a gidan gyaran hali.