Rundunar ‘yansandan jihar kano ta tabbatar da Cafke wasu Rikakkun masu yin kwacen waya da suka addabi Fasinjoji da kuma al’ummar kan titin stae Road da titin zariya, ta hanyar amfani da baburan adai-daita sahu mai dauke da Lambar KAROTA, KBY 0126
Wadanda ake zargin na ‘badda kama a matsayin matuka baburan adai-daita sahu sun hadar da Muhammad Jidda mai shekaru 20 sai Adamu sulaiman mai shekara 22 a Duniya Dukkanninsu mazauna unguwar Birgade
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin Rundunar yansandan jihar Kano, SP Haruna kiyawa da aka fitar, wanda yace kamen ya biyo bayan korafe-korafe babu kakkautawa daga al’ummar yankunan akan ayyukansu na yin kwace waya