Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da wasu shugabannin Kananan hukumomi guda Ukku, saboda zarginsu da yin balaguro zuwa kasashen ketare batare da samun wani izini daga bangaren zartarwa ko kuma majalisar dokokin jihar ba.
Shugabannin da aka dakatar sun hada da Shugaban karamar hukumar Birniwa Mubarak Ahmed sai Rufa’i Sunusi na karamar hukumar Gumel da kuma Umar Baffa wanda ke zama shugaban karamar hukumar Yankwashi, inda aka ce sunje kasar Rwanda batare da samun izini ba.
Daukar matakin da majalisar dokokin jihar ta Jigawa ta yi, ya biyo bayan kudirin da shugaban kwamitin kula da kananan hukumomi a zauren majalsiar, Aminu Zakari Tsubut ya gabatar akan shugabannin kananan hukumomin da abun ya shafa.
Ya ce zauren majalisar ya umarci shugabannin kananan hukumomin da kada su yi wata tafiya zuwa wani kafin gabatar da kudirin kasafin kudin sabuwar shekara, amma suka bijirewa umarnin.
Ya kuma baiyana halaiyar da suka nuna a matsayin rashin ‘Da’a da kuma nuna sakaci wajen sauke nauyin dake kan wuyan su.