An dakatar da shugaban karamar Hukumar Nasarawa Hon Auwalu lawan Shu’aibu daga kan kujerarsa har sai abunda hali ya yi.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewar sanarwar dakatar da shugaban karamar hukumar ta Nasarwa na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke dasa hannun kansiloli 11 na karamar hukumar.
Kansilolin sun bukaci dakataccen shugaban karamar daya mika ragamar tafiyar da mulkin karamar hukumar a hannun mataimakinsa Mu’azu Abubakar Adamu har zuwa lokacin da za’a kammala bincike.
Sun zarge shi da keta dokokin tafiyar da mulkin karamar hukuma, da yin almubazzaranci da rashin zama a ofis da sauran wasu lefuka.