Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara, Ya amince da Dakatar da Sarkin sabuwar Masarautar Birnin Yandoto, Alhaji Aliyu Marafa, bisa ga sarautar da ya bawa wani jagoran ‘yan ta’adda a yankin da ake nema ruwa a jallo, mai suna Adamu Aliero Yankuzo, wanda aka fi sani da Ado Alero.
Idan ba’a manta ba, a shekarar 2020 ne gwamnatin jihar Zamfara ta aiyana Alero a matsayin wanda take nema ruwa a jallo sakamakon yawaitar kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane da ake samu a yankunan dake zamfara da kuma jihar Katsina.
A ranar Asabar din data gabata ce, aka nada Alero a matsayin sarkin Fulanin Yandoto,Sai dai kuma yan sa’oi kadan da yin nadin, masarautar ta bada sanarwar dakatar da sarautar. Rahotanni na baiyana shugabanni ‘yan ta’adda daban daban ne suka halarci bikin bayar da sarautar da aka yi a lokacin.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar, Ta umarci Hakimin Yandoto Alhaji Mahe Garba Marafa daya rike harkokin tafiyar da masarautar kafin daukar mataki na gaba.