Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kano ta sanar da rufe cigaba da karbar kudin ajiya daga maniyyatan da ke shirin gudanar da aikin Hajjin 2023
Idan za a iya tunawa, hukumar ta sanya Naira milliyan 2 zuwa milliyan 2 da Rabi ga maniyyatan da ke da niyyar sauke farali a bana biyo bayan matakin gwamnatin Saudiyya na dawowa da Najeriya guraben kujeru dubu 95 tare da cire duk wasu ka’idojin COVID-19.
Da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Alhamis a Kano, Sakataren zartarwa na hukumar Jin dadin alhazai ta jihar Kano, Muhammad Abba Dambatta, ya ce daga yau hukumar ta rufe karbar duk wani sabon kudin ajiya daga maniyyata zuwa lokacin da za'a kammala aikin tantance wadanda suka riga suka biya naira miliyan biyu ko milliyan 2 da rabi.
Ya kuma musanta wata jita-jita game da ainihin adadin kudin kujerar aikin Hajjin bana.
An shirya fara jigilar maniyan Najeriya zuwa Hajjin 2023 a cikin watan Mayu nan da kwanaki 30 masu zuwa.