Jam’iyyar PDP ta sanar da dakatar da shugabanta na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, bisa zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa.
Shugabannin zartaswa na PDP a mazabar Igyorov da ke karamar hukumar Gboko a jihar Benue sune suka dakatar da Ayu.
Sakataren mazabar na PDP, Vangeryina Dooyum, ya ce an cimma wannan matakin ne bayan da shugabanni sukayi nazari kan babban zaben da aka kammala.
Idan za’a iya tunawa jam’iyyar PDP a matakin jihar ta Benuwe a karshen mako ta kada kuri’ar amincewa da Gwamna Samuel Ortom, wanda shugabancin zartarwa na kasa ya mikawa kwamitin ladabtarwa domin bincike kan shugaban jam’iyyar.
Anyi zargin cewa matakin ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na hana PDP daukar duk wani mataki na ladabtarwa akan Ortom har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.