Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya ce bai samu wani kason Kudi na ofishinsa ba a cikin watanni shida da suka gabata, inda ya ce yana gudanar da ofishin ne bisa sadaukarwa ta kashin kai da kuma masu fatan alkhairi.
Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Edo a birnin Benin.
Ya ce da ya kara yin fiye da hakan amma akwai takun saka tsakaninsa da gwamna Obaseki na tsawon watanni shida, al'amarin da ya sa ba a bada kadon kudin tafiyar da ofishin sa.
Shaibu ya ce shi dan takarar gwamnan jihar Edo ne a shekarar 2024, inda ya yi alkawarin ci gaba da gwagwarma da kafafen yada labarai wadanda suka ceci rayuwarsa a karkashin sojoji kafin dawowar mulkin dimokradiyya a shekara ta Alif 1999.