An dage lokacin rubuta jarabawar Qualifying ta manyan makarantun sakandire a jihar Kano, wadda aka tsara gudanarwa a jiya, har sai abunda hali ya yi.
Ma’aikatar Ilimi ta jihar kano ce ta sanar dage rubuta jarabawar bisa dalilai na yajin aikin da gamaiyyar kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka shiga a fadin kasa.
Sanarwar da kakakin Ma’aikatar Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar, Ta roki Dalibai da iyaye da su yi hakuri da yanayin da aka tsinci kai a saboda dage lokacin rubuta jarabawar.