Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta dage jigilar kaso na farko na maniyyata daga yau zuwa 3 ga watan gobe na Yuni.
Da yake karin haske game da hakan babban Sakataren Hukumar Muhammad Abba Danbatta ya ce, bitar aikin hajji a aikace da aka shirya gudanarwa jiya an maida ita zuwa ranar litinin
A cewar Danbatta, an kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin na bana.
Ya kuma bayyana cewa za a gudanar da bitar aikin hajji a aikace a sansanin Alhazai, inda masu ruwa da tsaki da maniyyatan zasu taru.
Haka kuma Babban sakataren hukumar jin dadin alhazai a jahar Kano Muhammad Abba Dambatta ya ce gwamnatin taraya ta bayar da tallafin akan Karin kudin jirgi da ya kamata su biya sakamakon yakin kasar Sudan.
Dambatta yace dala 703 a da za’a biya a matsayin Karin kudin jirgin amma kuma daga baya aka rage shi zuwa dala 100 bayan da gwamnatin taraya ta shiga cikin lamarin.
Sai dai, yace Karin kudin za’a cire shi ne daga cikin kudin guzirin alhazan na dala 800 inda za’a biya su dala 700…..
Danbatta ya kara da cewa daga cikin shirye shiryen da aka zuwa yanzu an biya kudin DTA,da kudin yellow card da sauran shirye shirye da suka kamata kafin tafiya aikin hajji.