An bukaci Wata Babbar Kotun Taraiyya mai zamanta a Abuja, data hana jam’iyyar APC maye gurbin sunan Kabiru Masari da wani mutum na daban, a matsayin Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Wasu kusoshin jam’iyyar biyu, sannan kuma wakilanta a zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka yi a kwanakin baya, Zakari Maigari da Kuma Zubainatu Mohammed ne suka garzaya gaban kotun, domin ganin ta hana hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta karbar canjin sunan dan takarar mataimakin shugaban kasa.
Bugu da kari sun bukaci kotu data yi bayani akan ko ya halatta a dokance, Kabiru Masari ya janye daga takarar mataimakin shugaban kasa, domin bawa jam’iyyar APCn damar canza shi da wani mutum na daban.
Idan har wannan shari’a tayi aiki, Ka iya shafar jam’iyyar LP wadda itama ta aiyana Doyin Okupe a matsayin Dan takarar Mataimakin ta na shugaban kasa, ammafa na wucin gadi.