Tsohon Dan Takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, Ambrose Owuru, Ya garzaya gaban kotun daukaka kara dake Abuja domin ganin an hana rantsar da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a matsayin sabon shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayun bana.
Owuru wanda ya nemi takarar a karkashin rusasshiyar jam’iyyar HDP, Ya bukaci kotun daukaka karar data hana ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami da hukumar zabe ta kasa rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban taraiyyar kasar nan.
Ambrose ya yi ikirarin shi ne wanda ya samu nasara a zaben shekarar 2019,kuma har yanzu wa’adin mulkinsa bai kare ba,kasancewar kotun koli har yanzu bata yanke hukunci kan karar da ya shigar gabanta ba, inda yake kalubalantar aiyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a wannan lokaci.
Kunshin takardar karar na dauke ne da sadarori har guda takwas,inda kuma yayi fatan za’a saurareta kafin ranar 29 ga watan gobe, To sai dai kuma kotun bata saka lokacin da zata fara zaman shari’ar ba.