Gabanin bikin ranar hawa Keke ta duniya da ake yi duk ranar 3 ga watan Yunin kowacce shekara, kungiyar masu hawa kekuna ta duniya, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kudaden tallafin mai wajen inganta harkar sufurin hawan keke wanda hakan zai temaka wajen dakile matsalar sufuri da tallafin cire tallafin man ya haifar.
Da yake ganawa da wakilinmu, Mataimakin Shugaban kungiyar , John Emmanuel ya bayyana cewar samar da ingantaccen tsarin sufuri, shi ne mafita ga jama’a a halin yanzu.
Ya kuma ce sakamakon cire Tallafin mai da aka yi , A halin yanzu hawan keke shi mafi rahusa ta bangaren sufuri, wanda yafi dacewa da yin zirga-zirga ta kimanin nisan kilomita 10 zuwa 15.
Ya bayyana cewa ana kan aiwatar da wani sabon tsarin inganta sufurin hawa kekuna na kasa, sannan ya bukaci Gwamnati da ta janye duk wani nau’in haraji da aka saka kan shigo da Keke a kasar nan.