Sakataren harkokin wajen Amurika, Antony Blinken ya tabbatar da cewar kwamdojin sojojojin sudan da basa ga maciji sun amince da tsagaita wuta na tsawon kwanaki ukku faraway daga yau Talata.
Kazalika ya ce gwamnatin Amurika na aiki da takwarorinta domin kafa wani kwamiti wanda zai tabbatar da an samu dauwamammiyar tsagaita wuta a kasar ta Sudan.
Rikici dai ya kaure tsakanin tsagin kwamandan sojin kasar da kuma dakarun runduna masu sanye da kayan sarki a kasar kwanaki goma da suka gabata, wanda hakan yayi sanadin mutuwar mutane 420 sannan kuma dubbai suka jikkata,kamar yadda wasu alkaluma da majalisar dinkin duniya ta fitar suka baiyana.