A ranar Talata ne Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da kudirin dokar daidaita kudin aure a jihar.
Kudurin dokar wadda Alhaji Abubakar Shehu na jam’iyyar APC dake wakiltar Yabo da Faruk Balle na jam’iyyar PDP dake wakiltar Gudu suka gabatar, an fara mika shi gaban kwamitin kula da harkokin addini na majalisar domin yin nazari a kansa.
Alhaji Abubakar Shehu wanda shi ne shugaban kwamitin, ya gabatar da rahoton a zauren majalisar a jiya, inda majalisar ta amince dashi.
Kudirin dokar dai ya tanadi kula da yadda ake kashe makudan kudade wajen auratayya ko bukin suna da sauran bukukuwa na al’ada da ake yi a jihar.