Shugaban kasar Amurika,Joe Biden ya yi alkawarin yin aiki tare da sabon shugaban kasa, Bola Tinubu ta fannin inganta tattalin arziki da kuma sha’anin tsaro.
Shugaba Joe Biden wanda ya turo tawaga mai karfi daga Amurika domin shaidar bukin rantsar da Tinubu, ya baiyana haka ne ta cikin wata sanarwa, wadda ke taya Tinubun murnar rantsuwar kama aiki da yayi a ranar litinin.
Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na yin aiki kafada da kafada da Tinubu domin karfafa zumuncin dake tsakanin Amurika da kuma nan Najeriya.
Joe Biden ya ce yana da kwarin gwiwa akan irin ingantattun manufofi dake tsakanin kasashen biyu.