On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ambaliyar Ruwan Sama Ta Cimma Kananan Hukumomi 31 A Kano - NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce ambaliyar ruwan sama ta cimma garuruwa akalla 225 a damunar bana cikin jihohin Kano da Jigawa al’amarin da ya haddasa asarar rayuka da dukiya mai yawa.

Bayanan na NEMA na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar kula da yanayi ta kasa NIMET ke ci gaba da gargadin yiwuwar fuskantar mamakon ruwan sama a wasu jihohin kasarnan galibi wadanda ke arewaci da tuni suka fara fuskantar mamakon ruwan sama ba kakkautawa.

A wani taron manema labarai da hukumar NEMA ta kira ranar asabar, shugaban hukumar reshen jihar Kano Dr Nuruddden Abdullahi ya bukaci al’umma su dauki matakan dakile barazanar ambaliyar.

Jihohin Kano da Jigawa na cikin  yankunan da ake fuskantar mamakon ruwa fiye da yadda suka saba a damunar bana, inda wasu yankunan ke ganin saukar ruwan ba kakkautawa tun daga watan Yulin da ya gabata.

Dr Abdullahi ya ce zuwa yanzu alkaluman da suka tattara ya nuna yadda ambaliyar ta shafi kananan hukumomi 31 a jihohin biyu tare da kashe mutane da rusa gidaje da kuma barnata dukiyar miliyoyi.

A cewar shugaban na NEMA, kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa sun kunshi Tudun Wada da Doguwa da Kibiya da Kiru da Gwale da Danbatta da Bagwai da kuma Ajingi baya ga Albasu da Shanono da Tsanyawa da Rimin Gado da kuma Dawakin Kudu dukkaninsu a jihar Kano.

A jihar Jigawa kamar yadda shugaban na NEMA ke shaidawa, ambaliyar ta shafi kananan hukumomin Kafin Hausa da Malam madori da Hadeja da Guri da Kirikasamma da Maigatari da Gumel da Birniwa da kuma Jahun baya ga Miga da Kiyawa da Birnin Kudu.

Shugaban na NEMA Nurudden Abdullahi ya bukaci al’umma a jihohin na Kano da Jigawa su dauka matakan da suka dace don kaucewa fuskantar ambaliyar musamman la’akari da gargadin hukumar NIMET wadda ta yi hasashen sake ganin mamakon ruwan sama a wasu jihohin Najeriya 19 ciki har da Kano da Jigawa tsakanin watan da muke ciki na Agusta zuwa Satumba fiye da yadda aka saba gani a irin lokacin.