On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Wasu Manyan Tituna A Kano

Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu manyan tituna a jihar, yayin da daruruwan motoci suka makale lalace inda mutane ke yin iyo a cikin ruwa mai zurfi sakamakon mamakon mamakon ruwan sama da aka wayi gari da shi a safiyar Alhamis.

Wakilinmu Abdurrahman Balarabe Isah wanda  ya ziyarci daya daga cikin wuraren da ambaliyar ta shafa a farkon titin zuwa  Zaria dake kusa da tashar mota ta Kano Line, ya ruwaito cewa zurfin ruwan ya shafe tayoyin yawancin motoci da suke yunkurin wucewa.

Ruwan da ya taru a wuraren da aka fuskanci  ambaliyar ya haura  guiwar wasu masu  tafiya a kasa da ke kokarin bi ta cikin ruwan, yayin da masu tuka babur mai kafa biyu da masu adaidaitasahu ke tura ababen hawansu domin gudun lalacewa.

Arewa Radio ta ruwaito cewa wasu manyan tituna da ke sassan birnin Kano sun fuskanci  irin wannan yanayi biyo bayan ruwan saman da aka wayi  gari da sanyin safiya.