An kwashe dubunnan daruruwan mutane a kasar Sin a wasu lardunan kudanci da gabashin kasar bayan da aka samu ruwan sama mai karfin gaske da ya haddasa ambaliya da zabtarewar kasa.
Ambaliyar ta haddasa tumbatsar koguna sannan kuma itace mafi muni da aka gani cikin tsawon shekaru 50.
Hotunan bidiyo da kafafen yada labarai na kasar suka fitar sun nuna yadda ake tsamo motoci da suka makale a tituna, da kuma ceto mutanen da igiyar ruwa ta ja.
An bukaci Mutanen da ke zaune a gefen kogi da su gaggauta tashi daga wajen.