Gwamnatin tarayya ta ce ana sa ran ambaliyar ruwan dam din kasar Kamaru zata afkawa jihohin Najeriyar nan da kwanaki bakwai.
Ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr Betta Edu, ta ce dukkan jihohin da ke kan hanyar kogin Benue na iya fuskantar ambaliyar ruwa cikin kwanaki bakwai masu zuwa sakamakon bude madatsar ruwan Lagdo a Kamaru.
Da take magana a wani taron manema labarai, Edu ta ce gwamnatin tarayya za ta aiwatar da manufofi daban-daban da ayyukan ceto da nufin dakile illolin da ambaliyar ruwan Lagdo zata haifar.
Sai dai ta bukaci kungiyar gwamnonin Najeriya da ta kara kaimi ta hanyar tabbatar da kwashe ‘yan Najeriya daga garuwan da ke fama da ambaliyar ruwa zuwa wurare masu aminci.