A garin garin babbba dake Karamar Hukumar garun Malam ta jihar Kano wasu 'yan ta'adda dauke da muggan makamai sun yi yunkurin garkuwa da mutane da dama ciki harda dagacin garin Alhaji Abdulmumin Mudi Zakari da tsakar dare.
A zantawarsa da wakilin Arewa Radio Bashir Faruk Durumin Iya mataimakin shugaban karamar hukumar garun malam Hon Aminu Haludu garun babbba ya tabbata da yadda bata garin suka shiga kauyen tare da yadda al'ummar gari da hadin gwiwa 'yan sanda da jami'an sa kai suka kubutar da Dagacin.
Hon Aminu ya kara da cewa bata garin sun fara shiga gidan wani Alhaji Habu daga nan kuma suka tafi gidan wani Alhaji Musbahu nan ma ba su samu nasarar ba.
Daga nan ne kuma suka shiga gidan Dagacin garin garun babbba Alhaji Abdulmuminu Mudi Zakari wanda a karshe aka kubutar da shi..
Wakilinmu na mu ya tuntubi kakakin rundunar 'yan Sandan Jihar Kano SP Abdullai Haruna Kiyawa ya tabbatar da harin.