On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Al'uma Sun Koka Kan Yadda Lalatacciyar Hanya ke Barazana ga Mata Masu Juna Biyu da kuma Tilastawa Yara Hakura da Makaranta

Lalataccen Titin Zuwa Joda, Karamar Hukumar Gabasawa

Al’umar garin Joda dake karamar hukumar Gabasawa sun koka dangane da lalacewar hanyar garin nasu, hanyar da suka ce ta kashe mutane da dama musamman mata masu juna biyu tare da tursasawa matasa da dama hakura da karatun su.

Tsahon shekaru 7 kenan suna fama da wannan matsala duk da tulin alkawura da yan majalisun su na jiha da na tarayya suka musu a lokutan da suka ziyarci garin domin neman kuri’un su a lokutan zabe daban daban.

Kolomita 8 ce kawai tsakanin Zugaci zuwa Kauyen Joda a karamar hukumar Gabasawa, sai dai hanyar ta kasance cikin wani hali na kakanikayi tsahon shekaru 7.

Da take magana da Arewa Radio, wata uwa, Hajia Aina’u Joda ta bayyana mana yadda hanyar ta dade tana barazana ga rayuwar mata masu juna biyu kafin a kai asibiti, dake da tazarar kilomita kadan daga kauyen.

Aina’u ta ce, “asibitin mu karami ne, baya karbar haihuwa. Sai mata sun je har asibitin Zakirai inda da yawa kan haihu a hanya, wasu ma basa karasawa asibitin da ran su.”

Barazanar da hanyar ke yi kan kara ta’azzara sa’ilin da damuna ta fadi tare da sanya shiga ko fita daga kauyen zama jan aiki ko da wani irin abun hawa mutum yake amfani da shi.

Duba da cewa sai sun yi tattaki zuwa garin zugaci domin zuwa makaranta a matakin babbar sakandare, da yawa daga cikin matasan kauyen sun hakura da karatun su, wanda ke da nasaba da yadda zirga zirga ke yi wuya lokacin damuna.

Yayin zantawar sa da Arewa Radio, wani matashi Abuzarrin Abdulmumin cewa yayi matsalar na tilsata musu hakura da karatu su rungumi wani abun na daban, tunda karatun ba zai dore ba.

“Ni da kanne na duk mun hakura da zuwa makaranta tun bayan da muka kammala karatu a mataki na karamar sakandire saboda ba za mu iya tafiyar kilomita 8 a wannan hanya zuwa garin Zugaci ba, inda a nan ne muke zuwa babbar makarantar sakandire.”

Matasan kan karkatar da hankulan su zuwa noma ko kuma hakar yashi a gabar Kogin Joda, sai dai hakan na fuskantar tasgaro sakamakon mutuwar da hanyar ta su ta yi.

Ita ma masana’antar hakar yashin, wacce a da ke tunkaho da samar da aiyukan yi ga dumbin matasan kauyen ta riga ta karye yanzu haka, sai dai dan abinda ba a rasa ba.

A cewar masu hakar yashin, kafin wannan lokaci suna iya cika tipopi sama da 100 dake hada-hada a yankin, ba kamar yanzu ba da suke fama da guda 5 ko kasa da haka, duk saboda matsalar hanyar.

Magaji Aliyu,  wanda guda ne cikin matasan da ke sana'ar yashi a yankin ya bukaci gwamnati ta kawo musu agajin gaggawa.

“Kafin hanyar ta lalace haka, akalla tipopi 100 zuwa 150 na zuwa gabar kogin Joda domin diban yashi a kowacce rana, amma yanzu sai sa’a muke samun guda 5, kuma masu hakar yashin nan suna nan a kauyen har yanzu, sun rasa aikin yi.”

Shima Tasi’u Ali, cewa ya yi, “hakar yashin ta kasance kashin bayan tattalin arzikin kauyen shekara da shekaru kuma durkushewar ta na cigaba da shafar walwalar su.”

JODA3

Shugaban matasan yankin, Baffa Abdulwahab Joda, ya koka kan yadda yace gwamnati ta yi watsi da wannan bukata ta su, duk da cewa Allah ya albarkaci garin nasu da arzikin noma da sauran albarkatun kasa.

“Allah ya albarkaci wannan gari namu da albarkatun kasa masu yawan gaske, musamman ma kasancewar mu a gabar kogin Joda, inda ake fita da yashi da darajar sa ta kai akalla naira miliyan 10 a kowacce rana, amma aka yi watsi da bukatun mu duk da cewa gwamnatin jiha da ta karamar hukuma na samun kudin shiga da mu”.

“Bayan wannan, muna noman rani da damuna kuma zan iya kurin cewa ba wani gari da ke samar da kudaden shiga a fadin Kano ta Arewa kamar garin Joda.”

Yayinda muka tuntube shi, dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Gabasawa, Hon. Zakariyya Abdullahi Nuhu yace tuni majalisar dokokin jihar kano ta amince da gini da kuma gyaran hanyar.

A cewar sa, yana nan yana bibiya domin ganin cewa aikin ya samu sahalewar majalisar zartarwa ta jiha, wadda yace ko a baya-bayan nan ta fitar da kudi domin fara aikin guda daga cikin titinan da ya gabatar da kudiri akan su.

“Allah da ikon sa, gwamnan jihar Kano ya sahale a fara guda daga cikin aiyukan titunan da na gabatar da kudirin su a majalisar dokoki ta jihar Kano kuma ina fatan za mu samu sahalewa domin kubutar da al’umar garin Joda daga wannan barazana da titin yake musu”.

Yayinda ake cigaba da jira, al’umar garin na Joda na kira ga yan majalisun su na jiha da na tarayya da su tuna alkawuran da suka musu na gyaran wannan titi lokacin da suke yawan neman zabe a lokutan baya.