Hukumar aikin hajji ta kasa, Ta baiyana rashin bacin ranta akan karancin Tantanina ga wasu Alhazan Najeriya kimanin dubu 10, a Muna, Wanda wani kanfanin kasar Saudiya ke aikin samar da Tantinan ga Alhazan Najeriya.
Shugaban hukumar, Alhaji Zikirullah Kunle ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Muna, Kazalika ya ce bai ji dadin yadda aka tsara ciyar da alhazan a filin Muna ba, kasancewar abincin bai wadata ba, sannan kuma ya zo a makare.
Ya kara da cewar tun da farko sunyi tunanin samun wannan matsala,wanda hakan tasa suka baiwa hukumomin saudiyya shawarar shigar dasu cikin tsarin ciyarwar, amma suka tilasta cewar suna da wani tsarin ciyarwa na bai daya.
Shugaban hukumar aikin hajji ta kasa, Ya ce tuni suka sanar da ma’aikatar aikin hajji da umarah ta saudiya koken da Alhazan Najeriyar suka yi, domin daukar matakin da ya da ce.
Sai dai a wani bangaren