Shugaban Masu rinjaye a zauren majalisar Wakilai Alhasan Ado Doguwa ya bi sahun masu zawarcin neman shugabancin zauren majalisar wakilan kasar nan.
A wata wasika ta baiyana kudirinsa da Alhasan Ado Doguwa ya aike da ita ga zababbun ‘yan Majalisar Wakialan, Ya baiyana cewar aniyarsa ta neman matsayin ya biyo bayan kishin da yake dashi na gina cigaban kasa.
A yanzu haka dai sakamakon baiyana aniyarsa ta neman kakakin zauren majalisar wakilai da ya yi, Yawan masu neman matsayin yanzu haka sun kai 11.
Baiyana burin nasa na zuwa ‘yan kwanaki, Bayan da wata babban kotun jihar Kano ta umarci babban lauyan gwamnatin jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan ya shigar da tuhumar zargin da ake yiwa Doguwa da hannu wajen aikata kisan kai da kuma kona wasu kadarori a yayin zaben shugaban kasa dana ‘yan Majalisar dokokin taraiyya da aka yi a kwanakin baya.