Ministar Kudi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin naira Tiriliyan 11 tare da sayar da wasu manyan kadarorinta domin samun kudin da za a cike gibin kasafin kudin shekarar 2023.
Ministar tace ana sa ran gibin kasafin kudin kasar zai zarta naira tiriliyan 12.42, idan har akaci gaba ta bayar da tallafin man Fetur a gaba dayan shekarar 2023.
Ministar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ta hallara gaban kwamitin kudi na majalisar wakilai domin gabatar da tsarin kashe kudi na matsakaicin wa'adi na shekarar 2023 zuwa 2025.
Yayin da take bayanin hanyoyin biyu da za a cike gibin ga kwamitin, Ministar ta ce hanya ta farko ta hadar da ci gaba da biyan tallafin man fetur har karewar shekarar 2023
Ta ce hanya ta farko an yi hasashen cewa gibin zai kai naira Tiriliyan 12.41 a 2023, idan haka bi wannan hanya gwamnati za ta kashe tiriliyan shida kan tallafin man fetur
Hanya ta biyu kuma ta kunshi ci gaba da biyan tallafi zuwa watan Yunin 2023, a wannan kuma gibin zai kai naira Tiriliyan 11.30, inda ake hasashen tallafin da za a biya zai kai naira tiriyan 3.3.