Tarayyar Najeriya ta sake jaddada bukatar daliban Najeriya da ke kasar Sudan su kasance a gida yayin da take ci gaba da shirye-shiryen kwaso su daga kasar mai fama da rikici.
A sanarwar da Ofishin Jakadancin Tarayyar Najeriya a birnin Khartoum, ya fitar a ranar Lahadi ya tabbatar da matakin gwamnatin.
Sanarwar ta shawarci daliban da su yi watsi da sanarwar da kungiyar dalibai ta kasa NANS a Sudan ta fitar, inda ta yi kira ga daliban da su hadu a ofishin NANS kuma su kawo dala 100 ko dala 200 domin kwashe su.
Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu yana da hadari a fara tattaki zuwa kan iyakokin Sudan ba tare da samun tabbacin tsaro daga hukumomin Sudan ba.
An kashe daruruwan mutane tun bayan da aka fara gwabza fada tsakanin dakarun janar-janar guda biyu a birnin Khartoum.