On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Akwai Bukatar Shigar Da Kwarewa Harkar Siyasar Dandalin Sada Zumunta Da Sojojin Baka - Isa Nasidi

Wani matashin mai bincikekan harkokin sadarwa Isa Nasidi ya bukaci ‘Yan Siyasa a Najeriya su guji yin Kalaman batanci dana tunzura jama’a da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya kafin da lokacin da kuma bayan zabuka.

Isa Nasidi wanda kuma dalibin digiri na Uku ne a jam’iar Najeriya dake Nsukka ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da manema labarai dangane da wasu litattafai guda 3 da ya wallafa  akan kalaman ‘Yan Siyasa da Masu magana a gidajen Radiya da ake kira Sojojin baka  da kuma kalamai a kafafen sada zumunta na zamani.

Yace a binciken da ya gudanar a hukuncin da Kotuna daban-daban suka Yanke a jihar Kano ya gano cewa sau da yawa ana samun sojojin baka da lefin yin Kage da muzanta abokan hamayyarsu na  siyasa, yana mai cewa a wasu lokuta ana amfani da sojojin bakan ne wajen cimma muradan siyasa domin su kare ko suyi ziga  ko su kushe wani sakamakon Zalakar zance da suke da shi.

“Zarge-zargen da ake musu a Mafi yawan lokaci gaskiya ne domin na bibiyi wasu hukunce-hukuncen kotuna a nan Kano inda na gano cewa an kamasu da laifin yada karairayi da cin zarafin mutane da Kage”, inji shi.

“Na ziyarci hukumar NBC dake kula da  gidajen Radio da Talabijin na gano cewa wadannan sojojin  baka sun sha jawowa gidajen Radiyo tara ko gargadi” Acewar Nasidi.

Isa Nasidi ya kara da cewa ‘yan jarida na da rawar da zasu taka na tabbatar da ta ce dukkan abubuwan da mutane yakamata su saurara a Radiyo tare da taka burki ga Yan Siyasa masu kalaman da zasu iya bata sunan wasu, duk da cewa a wasu lokutan manyan Yan Siyasa ne ke matsa musu domin ganin sun yi abin da ya sabawa kaida.

Har ila yau, Isa ya ce a littafin da ya rubuta yayi bayanin menene labarai karya  da yadda ake gane su da kuma ilolinsu ga al’umma, yana mai cewa an wallafa shi da turanci da kuma Hausa sannan an maida shi cikin sautin murya ta yadda al’umma zasu iya saurara Musamman ga wandanda basu iya karatu da rubutu ba ko ga masu bincike.

Marubucin wanda kuma dan jarida ne ya shawarci ‘yan jaridu a Kano dama Nageria da su tabbatar da tantancewa gami da tace abubuwan da zasu  je kunnen jama’a la’akari da irin gudun mawa da tasirin su a tsakanin al’umma.

Ya kuma bada sharwarin ga  gwamnatoci da hukumomin da ma'aikatu da masu ruwa da tsaki domin dakile matsalar,ta hanyar shigar da kwarewa.

Daga bisani yace kofarsa a Bude take ga hukumomi da ma’aikatu ko dai-dai kun mutane domin hada kai wajen isar da muhimman abubuwan dake ciki  ga al’umma domin amfanarsu.