On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Akwai Bukatar Ayyana Dokar Ta 'Baci Akan Zazzabin Cizon Sauro - Majalissar Wakilan Najeriya

Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan cuta mai karya garkuwar jiki da  tarin fuka da zazzabin cizon sauro, dan majalisa Amobi Ogah ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta-baci kan cutar zazzabin cizon sauro.

Ya bukaci hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar domin tunawa da ranar Zazzabin cizon sauro ta duniya ta 2023.

Ana bikin ranar zazzabin cizon sauro ta duniya a duk ranar 20 ga watan  Agusta.

Taken bikin na 2023 shine, yaki da  sauro mai hatsarin kisa a  duniya.

Ogah ya ce duba da irin barazanar da cutar zazzabin cizon sauro ke yi wa al’umma, dole ne a yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kawar da sauro mai kisa.