Hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa UBEC ta ce samun hakikanin adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya ba zai yiwu ba sai an yi kidayar jama’a.
Sakataren zartarwa na UBEC, Hamid Bobboyi, ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin a wajen taron karrama marigayi GidadoTahir.
A baya dai anyi kiyasi daban-daban dangane da adadin yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya.
Sai dai yayin da yake magana kan al’amarin, Bobboyi ya yi kira ga hukumar kidaya ta kasa NPC da ta gudanar da kidayar 2023 domin baiwa UBEC damar samun ingantacciyar kididdiga.