Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya dora alhakin karancin man fetur da ake fama da shi a fadin kasar nan kan gazawar jam’iyyar PDP wajen gyara matatun man Najeriya a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulkin kasar nan.
Oshiomhole, wanda ya kasance Mataimakin babban Daraktan yakin neman zaben Tinubu da Shettima, ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi dashi kai tsaye a gidan Talabijin na channels.
Ya ce dole ne a tambayi waye ya lalata matatun, yaya yanayin matatun ya kasance a 1999 da kuma daga shekarar 1999 zuwa 2015 lokacin da PDP ta shafe shekaru 16 tana mulki.
A cewarsa, daya daga cikin manyan kalubalen da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fuskanta a wancan lokaci shi ne na man fetir a kasar nan.