Tsohon na hannun damar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima, Yace ba abun mamaki bane a sace shugaban kasa, La’akarin da yadda matsalar tsaro ke kara dagulewa a kasar nan.
Buba Galadima na wadannan kalamai ne a matsayin martani kan halin da tsaron kasa ke ciki a yanzu yayin hirarsa da Sashin Hausa na BBC.
Yace idan har yan Ta’adda zasu iya kutsa kai gidan gyaran hali na kuje, to babu shakka shi kansa shugaban kasa Buhari bai tsira ba.
Ya kara da cewa mudddin ba’a dauki matakan da suka dace ba, nan bada jimawa ba za’a iya dauke shugaban kasar duba da yadda ake yiwa harkokin tsaro rikon sakainar kashi.
Buba Galadima yace a farkon hawan mulkin Buhari kowa na tsoronsa saboda tunanin zai tabuka wani abun kirki , amma daga karshe sai aka gane tsumman maciji ne.
Ya kuma kara da cewa babu abunda shugaban kasar zai iya yi, wanda hakan tasa wasu manyan jami’an gwamnati ke sace bilyoyin kudade daga aljihun gwamnati.